Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yan Najeriya sun yi zanga-zanga a London

Daruruwan 'yan Najeriya mazauna Ingila sun gudanar da wata zanga-zangar lumana don nuna adawa da janye tallafin man fetur din da gwamnatin Najeriyar ta yi. Masu zangar-zangar sun taru ne a dandalin Trafalger da ke tsakiyar London inda suka rera wakokin kin amincewa da matakin, inda daga bisani suka je ofishin jakadancin Najeriyar don mika koken su.