Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An zargi sojojin Amurka da yin fitsari kan mayakan Taliban

Rundunar sojin Amurka tace tana bincike a kan wani hoton bidiyo wanda ke nuna mutane hudu sanye da kayan sojojin kasar suna fitsari a kan gawarwakin wasu mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan. Wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurkar ta Pentagon ya ce hoton bidiyo mai ta da hankali ne matuka, kuma halayyar sojojin ba ta dace ba.