BBC navigation

Hotuna: Burin gasar Olympics

An sabunta: 16 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 17:17 GMT

Burin gasar Olympics

 • Usain Bolt, Dan Jamaica kuma wanda ake saran zai yi tsere a gasar Olympics ta London a 2012

  "Ban riga na gawurta ba.Ina kan hanya ne amma sai naje London na burge mutane".

  Usain Bolt , dan tseren Jamaica wanda zai fafata a gasar Olympics ta London a 2012

  Usain Bolt na daga cikin 'yan wasa a duniya da BBC ke lura da shirye shiryensu na London 2012. Shin wata bajinta suka yi a 2011? Sai dai ba za a iya tuna irin haskakawar da Usain Bolt ya yi a 2011.An dakatar dashi a gasar tseren mita dari ta duniya saboda kuskuren da yayi wajen fara tseren. Amma dai dan Jamaica din ya kare kofinsa na mita 200 sannan ya kafa tarihi a gasar hadaka ta 4x100. Ya kamalla kakar wasan data wuce a matsayin wanda ya kafa tarihin mita 100 a cikin dakikoki 9.76 a Brussels.

 • Nader el Masri, mai tseren dogon zango daga Gaza kuma shima zai fafata a gasar Olympics ta London

  "Ina da koci amma babu wanda ya kaini a Gaza.Dole ne in dunga motsa jiki da kaina".

  Nader el Masri, mai tseren dogon zango daga Gaza kuma shima zai fafata a gasar Olympics ta London

  El Masri ya nuna cewar shi gwarzo ne bayan da ya lashe tseren fanfalaki na farko a Gaza. Bapalasdinen kuma ya taba yin tseren a cikin mintuna 14 da dakika 21a tseren mita 5000 wato kasa da mintuna 13 da dakika 27 da samun gurbin zuwa gasar Olympics.

  An bayyanawa El Masri cewar ba zai samu gagarumar tarbaba a London 2012.

 • Alistair Brownlee, zakaran gasar triathlon na Birtaniya.

  "Wannan rana ce ta musamman tunda na samu nasara a wasanni biyu! Mutane da dama ba zasu iya cewa komai akai ba".

  Alistair Brownlee, shine zakaran Birtaniya a gasar triathlon ta duniya kuma zai je gasar Olympics ta London a 2012.

  An baiwa Alistair ya zama zakaran duniya a watan Satumbar 2009. Sannan kuma ya lashe gasar Turai a shekara ta 2012.

 • Haider Rashid dan Iraki wanda ake saran zai je gasar Olympics ta London a 2012

  "Ina da bukatar yin kokari don samun gurbi saboda ina da bukatar haka".

  Haider Rashid dan Iraki wanda ake saran zai je gasar Olympics ta London a 2012.

  Haider Rashid ya shaidawa Mathew Pinsent a gasar duniya a Slovenia a 2011 cewar yanason ya je London. Rashid ya kamalla a matsayin ta 27 cikin 34 kuma yanada damar tsallakewa a watan Afrilu 2012.

 • Olga Kharlan, 'yar wasan Olympic na Ukraine

  "Kakana ya ce na samu damar da basu taba samu ba a tsaron rayuwarsu".

  Olga Kharlan, 'yar wasan Olympic na Ukraine

  Shekara ce da Olga yayi kane kane a Turai amma sai ya kasa nuna karfinsa a duniya. Ta kasance zakaran Turai a Sheffield amma ya samu tagulla a gasar duniya a Italiya. A kashin kanta, zata iya samu kudi wajen gina gidan kanta don ta fita dag gidan iyayenta mai daki guda.

 • Julien Absalon, dan Faransa mai gasar hawa tsauni a keke

  Julien Absalon, Dan Faransa mai gasar hawa tsauni a keke kuma wanda ake saran zai je gasar Olympics a London

  Faransawa sun saba yin kakagida a gasar amma a 2011 Julien kyautar azurfa ya samu a gasar Turai sai kuma tagulla a gasar duniya. Amma dai shine ya lashe gasar Faransa abinda ya tsallakar dashi zuwa gasar Olympics a London a 2012 a wasannin share fage a Essex.

 • Majlinda Kelmendi 'yar Judo daga Kosovo

  "Na ki amincewa da bukatar wasu manyan kasashe masu karfi saboda in wakilci Kosovo kuma banason wani ya shaida mani hakan ba zai yiwu ba".

  Majlinda Kelmendi 'yar Judo daga Kosovo kuma wanda ake saran zai je gasar Olympics ta London

  Ta samu tabbacin tsallakewa zuwa gasar Olympics ne tun a watan Oktoba lokacinda Majlinda ta samu kyautuka zinare uku a wasu makwanni. Nasararta ta sa ta koma ta uku a Judo a duniya a nauyin kilogram 52. A shekara ta 2012, Majlinda na saran ta kasance 'yar wasa ta farko da zata wakilci Kosovo a gasar Olympics-matsala mai girma saboda hukumar IOC bata amince da kasarta ba

 • Jehue Gordon, dan wasan Hurdle daga

  "Bai kamata mutum ya dakatar da kanshi ba saboda yanayin da yake ciki. Saboda kai dan kyauye neba dole bane ka nuna cewar kai dan kyauye ne".

  Jehue Gordon, dan wasan Hurdle daga Trinidad kuma wanda ake saran zai je gasar Olympics ta London

  A gasar Diamond a watan Mayu, Jehue yayi gudu a cikin dakikoki 49.09 wato lokacin daya bashi damar tsallakewa zuwa gasar Olympics amma kuma daga bisani sai ya kasa tsallakewa zuwa gasar tseren hurdle na mita 400 a gasar cin kofin duniya. Amma bayan mako guda sa yayi gudu a cikin dakikoki 48.66 wanda ya bashi kasancewa na 13 a shekarar a fadin duniya

 • Linet Masai,'yar tseren dogon zango ta Kenya

  Linet Masai,'yar tseren dogon zango ta Kenya wacce ake saran zata je gasar Olympics a London

  Linet ta soma shekarar ce ta hanyar lashe tseren fanfalaki a Edinburgh. Ta wuce 'yar uwarta daga Kenya Vivian Cheruiyot da dakikoki takwas wato tamkar ramuwar gayyar abinda aka yi mata a gasar duniya. A shekaru uku a jere Linet ta kasance ta biyu. Ta kuma kare kofinta na tseren kilimita 10 a New York amma a gasar duniya a Koriya ta sha kashi inda Vivian Cheruiyot ce ta lashe tseren.

 • Luol Deng dan wasan kwallon kwando daga Birtaniya

  "Naji dadi duka muna nan, duka wadanda suka fice.Na ji dadi iyaye ma sun ga wannan ranar, sadaukarwar da suka yi yayi amfani".

  Luol Deng dan wasan kwallon kwando daga Birtaniya kuma wanda ake saran zai je gasar Olympics ta London

  Luol Deng zai kasance a London bayan da hukumar kwallon kwando ta duniya ta amincewa Birtaniya cewar zai iya buga mata. Bayan samun kyautar gwarzon dan kwallon kwando na duniya, Luol Deng ya haskaka a tawagar Birtaniya a gasar Turai a watan Satumba.Luol ya ziyarci kasarsa ta asali wato Kudancin Sudan a karon farko tun da ya fice yana yaro saboda yakin basasa.

 • MC Mary Kom, yar danbem India kuma wacce ake saran zata je gasar Olympics ta London a 2012

  "Abu ne mai sosa rai data barmu kafin tiyatar da aka yiwa danta amma tayi mani alkawarin zata samu nasara, nayi murna tayi hakan".Omler Kom

  MC Mary Kom, yar danbem India kuma wacce ake saran zata je gasar Olympics ta London a 2012

  Ta fuskanci kalubale matuka akan batun lafiyar danta da kuma yadda zata dinga horo. A dai dai lokacin da za a yiwa danta tiyata, Mary Kom ta lashe kofin nahiyar Asiya wato kofinta na takwas a cikin shekaru 12. A watan Nuwamba, ta shiga gwajin Olympics inda itama ta bayyana raayinta akan batun tilastawa mata saka kampai." Masu tennis mata suna saka duros haka ma 'yan wasan Badminton

 • Merlin Diamond 'yar tseren Namibia

  "Idan kana bukatar rayuwa mai inganci kuma kanada bukatar yin wani abu, dole ne sai ka sadaukar da kai akan abubuwa da dama".

  Merlin Diamond 'yar tseren Namibia wacce ake saran zata je gasar Olympics ta London a 2012

  A shekara ta 2011 Merlin Diamond ta haskaka. A farkon shekarar, tayi tafiya zuwa Birtaniya a karon farko don ziyararta filayen Olympics a gabashin London. Daga nan sai ta tafi ta bar iyalanta da kawaye don tayi horo na musamman a tsibirin Mauritius. Koda yake dai tayi sa'ar samun tallafi daga hukumar IOC, amma dai kayayyakin horo basu da kyau kuma ta fuskanci kewa. Data koma Namibia ta kara kiba kuma da kyar take gudu wanda keda wuya ta tsallake zuwa gasar London.

 • Rohullah Nikpai, dan wasan taekwondo daga Afghanistan

  "Ta hanyar samun kyautuka, ina saran zan kawo zaman lafiya da cigaba a kasata."

  Rohullah Nikpai, dan wasan taekwondo daga Afghanistan wanda ake saran zuwa gasar Olympics ta London a 2012

  Shine kadai dan kasar Afghanistan daya taba samun kyauta a Olympics kuma ya shirya bada mamaki. Rohullah ya samu gurbin zuwa Olympics daga Afghanistan bayan ya samu kyautar tagulla a ma'aunin kilogram 68 na gasar kasashen Asiya. Daga bisani sai ya samu kyautar tagulla a gasar taekwondo ta duniya a watan Mayu a Koriya ta Kudu.

 • Shawn Johnson wata 'yar tsalle-tsalle daga Amurka

  "Da aka zabe ni, sai na fashe da kuka. Sake kasancewa tare da tim din nada mahimmanci sosai. Inata fadin cewar gwaji ne kawai, amma a yanzu ya tabbata."

  Shawn Johnson wata 'yar tsalle-tsalle daga Amurka wacce ake saran zata je gasar Olympics ta London

  Bayan hadarin data yi a shekara ta 2010, Shawn Johnson ta sake shiga cikin tawagar Amurka a 2011. Koda yake dai ba a zabe ta ba a cikin wadanda zasu je gasar duniya a Tokyo. Amma kuma ta lashe gasar kasashen Amurka. Kamfanin Nike ya cigaba da bata talla har zuwa watan Yuni kuma ta shirya shiga wasanni share fage na Amurkawa a San Jose.

 • Wu Minxia, 'yar wasan ninkaya daga China

  "Ni ce wacce tafi shekaru a cikin tawagar a don haka ina tare da kannena, sauran suna kira na sister Xia."

  Wu Minxia, 'yar wasan ninkaya daga China kuma wacce ake saran zata je gasar Olympics ta London a 2012

  Wu Minxia da abokiyar wasanta He Zi sun lashe gasar duniya kafin su samu gurbin zuwa gasar Olympics ta London. Bajintarsu ta basu kyautar zinare a gasar duniya a Shanghai a karon farko.

  Amma duk da haka, sun kara samun zinare a gasar China a watan Satumba. Tun lokacin da Guo Jingjing tayi ritaya. Wu ce ta zama zakakura a China kuma ta samu kyautuka da dama.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.