Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mutane da dama sun rasu a rikicin kwallon kafa a Masar

Wasu magoya bayan kwallon kafa a Masar sun bayyana yadda rikici ya faru a filin wasa na Al-Masri inda akalla mutane 74 suka rasa rayukansu. Lamarin dai ya haifar da suka ga hukumomin tsaron kasar ta kowacce fuska.