BBC navigation

Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano

An sabunta: 8 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 14:05 GMT

Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano

 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Mutane a unguwar Gado da ke garin Mariri na birnin Kano a Arewacin Najeriya na ci gaba da zaman dar-dar bayan da aka shafe sa'o'i da dama ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu mutane da suka buya a cikin wani gida. Hotuna: Yusuf Yakasai
 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Rahotanni daga yankin sunce tun misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin ake musayar wuta inda kuma aka wuce karfe goma sha biyun daren ba'a daina ba.
 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai wanda ya ziyarci gidan da abun ya faru, ya ce an yi fata-fata da gidan. Jami'an tsaro sun ce sun gano bindigogi da harsashai da kuma abubuwan hada bam.
 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Jami'an soji sun ce sun kashe 'yan bindigar da ke zaune a gidan, yayin da suka kama mutane biyar. Wannan wani sashi ne na jikin mutum.
 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Lamarin dai yasa wasu daga mutanen unguwar tare da iyalensu sun kauracewa gidajensu, yayin da wasu kuma suka kwana cikin fargaba da tashin hankali.
 • Hotuna: Zaman dar-dar a garin Mariri na Kano
  Harin da jami'an tsaron suka kai unguwar ta Mariri dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari ofishin 'yan sanda na Sharada, inda suka jefa wani abin fashewa da ya kona ofishin kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa BBC tare kuma da raunata akalla dan sanda daya.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.