Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kididdiga: Talauci ya karu a Najeriya

Image caption Matalauta a Jihar Sokoto, Najeriya

A wani rohoton da ta fitar a farkon makon nan, Hukumar Kididdiga ta Kasa a Najeriya (National Bureau for Statistics) ta ce talauci ya karu a kasar idan aka kwatanta da shekara ta 2004.

Hukumar ta bayyana cewa fiye da kashi sittin cikin dari na 'yan kasar ne ke rayuwa a kasa da kwatankwacin dalar Amurka daya a kowacce rana, wato mutane kusan miliyan dari ke nan, daga cikin dukkan 'yan kasar kusan miliyan dari da 60.

Rahoton ya kuma ce a yankin arewacin kasar ne talaucin ya fi kamari.

Hukumar ta ce amfani da kiddigar zai iya taimakawa gwamnatoci su yi gyare-gyare a kan abubuwan da suka shafi ci gaba.

Wannan ne batun da muka tattauna a kai a shirin Ra'ayi Riga na wannan makon.