BBC navigation

Tarihin Gidan rediyon BBC

An sabunta: 28 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 14:12 GMT

Tarihin Gidan rediyon BBC

 • Gidan rediyon BBC mai watsa shirye-shiryensa zuwa kasashen waje 'BBC World Service' na bikin cika shekaru 80 da kafuwa. Latsa nan domin ganin muhimman abubuwan da suka faru a tarihi.

 • Ranar farko ta watsa labarai

  An kafa sashin BBC na Empire Service a watan Disamban 1932, ta hanyar gajeran zango wanda ke bayar da damar watsa bayanai zuwa dogon zango. Duk da cewa Darakta Janar na BBC John Reith ya yi hasashen cewa shirye-shiryen ba za su kayatarba, shirin da aka watsa daga da dakin watsa labarai na Broadcasting House ya samu kyakkyawan yabo.

 • Jawabin sarki

  Kwanaki shida bayan bude tashar, sai sarki King George V ya yi jawabi kai tsaye daga Sandringham. Marubicin nan Rudyard Kipling ne ya rubuta jawabin. An saurari jawabin sarkin a sassa daban-daban na duniya. Darakta Janar na BBC ya bayyana jawabin da cewa wata babbar nasara ce ga BBC.

 • Kirkiro sabbin harsuna

  Yakin duniya na biyu ya haifar da sauya wa tashar suna - inda ta koma tashar kasashen waje 'Overseas Service' a watan Nuwamban 1939 tare da bude sabbin tashoshi na harshen Larabci da Spaniya ga Latin Amurka, Jamusanci Italiyanci, Faransanci, Afrika, Spaniyanci ga Turai da kuma Portugal ga Turai. A karshen 1940, BBC na watsa shirye-shiryenta a harsuna 34.

 • Komawa Bush House

  Rashin isasshen wuri ga sauran harsunan kasashen waje a Broadcasting House da fashewar wata nakiya ta Jamus a wajen ginin a 1940, ta haifar da gobara wacce ta lalata ginin sosai. Harsunan da ke watsa shirye-shirye zuwa kasashen Turai sun koma zuwa Arewacin London. Sannan a 1941 suka koma Bush House a tsakiyar birnin London inda ake biyan fan 30 a kowanne mako a matsayin kudin haya.

 • Dauko labaran yaki

  Wakilan BBC masu aiko da labaran yaki kamar CD Adamson na wannan hoton, suna aiko da rahotanninsu daga filin daga ta faifan CD. Masu aiko da rahotannin kan aika da faifan rahotannin na su zuwa birnin Alkahira tare da taimakon sojoji domin aika wa London.

 • BBC da yakin cacar baki

  A 1946, ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta nemi BBC ta bude sashin Rasha kuma an fara watsa labarai da Rashanci bayan wata guda. Da farko jama'a a Rasha na iya sauraran shirin ba tare da wata matsala ba, amma bayan da yakin cacar baki ya zafafa, sai gwamnatin Rasha ta fara daukar mataki. An rinka samun cikas wurin sauraron shirye-shiryen BBC a Rashan abinda ya sanya BBC ta kara karfin na'urorinta.

 • Tsage gaskiya

  A lokacin da ake rikicin Suaz a 1956, Fira Ministan Burtaniya Anthony Eden ya yi amannar cewa sashin Larabci na BBC zai rinka bayar da rahotannin da za su goyi bayan sojojin Burtaniya. Sashin ya tsaya a tsakiya ba tare da nuna san kai ba, kuma ya samu goyon bayan Darakta Janar Ian Jacob duk da cewa an shaida wa ofishin cewa ministoci na shirin rage kudaden da ake baiwa BBC da fan miliyan guda.

 • Sakonni na musamman

  Bayan da dakarun Tarayyar Soviet suka murkushe boren Hungry a 1956, sashin Hungry na BBC ya watsa hira da wasu 'yan gudun hijira da suka bar kasar zuwa Burtaniya. 'Yan gudun hijirar sun yi amfani da wasu alamu na bar da kama domin kada mahukuntan Hungry su gane danginsu.

 • Bunkasar rediyo

  Amfani da rediyo ya bunkasa a shekarun 1960, sakamakon kirkiro karamar rediyo mai amfani da batir. Amfani da rediyo ya ninka sau uku tsakanin shekarun 1955 zuwa 1965 a Gabashin Turai, sannan ya karu matuka a yankin Gabas ta Tsakiya, China, Afrika da kuma India. A watan Mayun 1965, Overseas Service ta zamo World Service.

 • Sauye-sauyen harsuna

  Tarihi ya nuna cewa BBC ta watsa shirye-shirye a cikin harsuna 68. Yawancin wadannan harsunan na zuwa ne su tafi, ciki harda Maltese, Gujarati da dai sauransu. Faduwar bangon Berlin ta sa an rufe harsunan Turai da dama domin mayar da hankali kan yankunan da suka fi muhimmanci. Wasu rage-ragen da aka kuma yi sun sa adadin harsunan a yanzu ya zamo 28, yawancinsu suna watsa shirin ne ta hanyar Internet kawai.

 • Sauya akalar labarai

  Bayan rugujewar Tarayyar Soviet a farkon shekarun 1990, sai wani sabon zaman dar-dar ya barke a yankin Gulf. A ranar 2 ga watan Agustan 1990, dakarun Iraqi karkashin jagorancin Saddam Hussein suka mamaye Kuwait. Lokacin da dakarun hadin gwiwa suka fara kai hari kan Iraqi a watan Janairun 1991, sai BBC ta sauya akalar shirinta, ta koma kawo rahotanni da sharhi kai tsaye a karon farko.

 • Yabo daga Gorbachev

  A lokacin da aka tsare Mikhail Gorbachev na kwanaki uku lokacin da aka yi juyin mulki a 1991, hanya daya da yake sanin halin da duniya take ciki, ita ce ta sauraron gidan rediyon BBC. Tsohon Manajan BBC John Tusa ya kan tuna wani taron manema labarai lokacin da Mr Gorbachev ya bayyana BBC da cewa ita ce kan gaba a duniya.

 • Muhimmancin Rediyo

  Rediyo ta taka rawar gani a yakin basasar 1994 da aka yi a kasar Rwanda. Gidan rediyon Mille Collines na Rwanda ya taimaka wurin cusa kiyayya kan 'yan kabilar Tutsi da kuma 'yan Hutu masu matsakaicin ra'ayi. Amma BBC ta taimaka wajen samar da daidaito. Masu shirya shirye-shirye daga sashin Faransanci da Swahili sun yi aiki tare da kungiyar agaji ta Red Cross domin taimakawa miliyoyin mutanen da suka bar gidajensu. Daga bisani an fadada sashin ta hanyar kafa sashin Great Lakes.

 • Martani cikin rudani

  Hare-haren da aka kai ranar 11 ga watan Satumba a cibiyar kasuwanci da ke New York, ya sa an shiga wani irin yanayi na kidimewa a Bush House. Wannan martani ne da ba a saba ganin irinsa ba a wani lokaci na musamman. Editan da ke aiki a ranar Rachel Harvey ta mike daga kan kujerarta, ta nemi ma'aikata da su kwantar da hankalinsu, sannan ta zayyana yadda za ta bullowa al'amura a lokacin da suke faruwa.

 • Alan Johnston

  Bude sashin talabijin

  Bayan aiki na wani dan lokaci a 1990, gidan talabijin din Larabci na BBC ya sake fara aiki a watan Maris na 2008, sannan gidan talabijin na sashin Parisa ya bi bayansa a 2009. An fara watsa shirin talabijin zuwa kasashen duniya a harshen Turanci a 1991 da World Service TV wacce a yanzu ake kira BBC World News.

 • Alan Johnston

  Garkuwa a filin daga

  An kame wakilin BBC a zirin Gaza Alan Johnston a watan Maris na 2007 sannan aka yi garkuwa da shi. An sako shi bayan shafe kwanaki 114. A tsawon wannan lokaci, shirin BBC na World Have Your Say ya rinka watsa sakonnin goyon baya daga masu saurare a koda yaushe. Wannan ba shi ne karon farko da ma'aikatan BBC ke shiga cikin hadari ba. An tsare wasu da dama ko an muzguna musu ko iyalansu. Wasu ma sun rasa rayukansu. Aiko da rahotanni na ci gaba da kasancewa aiki mai hadari.

 • Juyin juya halin internet

  A lokacin yujin-juya halin kasashen Larabawa, shafukan sada zumunta sun zamo hanyoyin samun labarai ga 'yan jarida. Bayanai daga shaidu, da hotuna da bidiyo sun rinka fitowa daga yankin. Amfani da irin wadannan bayanai yana da muhimmanci wurin shigar da masu sauraro cikin labari. Shafukan sada zumunta na ci gaba da kasancewa hanyar da BBC ke samu da kuma watsa labaranta.

 • BBC Broadcasting House

  Sabon gida

  A shekara ta 2012 BBC World Service za ta sake komawa Broadcasting House bayan shekaru 71, zuwa wani dakin watasa labarai na azo-a-gani. Ma'aikatan World Service za su hadu da sauran takwarorinsu na BBC - da masu aiki kan shafukan internet da kuma talabijin - domin samar da ingantattun labaran duniya.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.