BBC navigation

Hotuna: Dan bindiga ya kashe Yahudawa

An sabunta: 19 ga Maris, 2012 - An wallafa a 16:36 GMT

Hotuna: Dan bindiga ya kashe Yahudawa

  • Wani dan bindiga akan babur ya kashe wasu yara uku da wani babba a wata makarantar 'ya'yan Yahudawa dake kudancin birnin Toulouse a Faransa.
  • Wani mai gabatar da kara Michel Valet ya ce wani mutum dan shekara 30 da 'ya'yansa biyu maza, daya dan shekara uku , dayan kuma dan shekara shida ne aka kashe tare da wani yaro dake da shekaru takwas zuwa goma.
  • An kai harin ne a lokacin da iyaye ke kai yaransu makarantar ta Ozar Hatorah dake yankin Joliment na birnin gabannin fara karatu.
  • Wata jarida a birnin Toulouse, La Depeche ta ce anyi harbin ne a inda ake ajiye yara 'yan makarantar share fagen firamare da na firamare.
  • 'Yan sanda sun ce kisan yayi kama da kisan da aka yiwa wasu sojoji uku a lokaci daban daban a makon jiya a Faransa.
  • Ana tunanin daya daga cikin bindigogin da akayi harbin da su, da shi akayi amfani wajen kashe sojoji uku a garin Montauban a ranar Alhamis.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.