Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wa ya fi karuwa a hulda tsakanin China da Afrika

Image caption Babban dakin taron kungiyar tarayyar Afrika da China ta gina a Habasha

An kammala wani taro na kwanaki biyu akan kasuwanci tsakanin China da kasashen kungiyar habbaka tattalin azikin yammacin Afurka, wato ECOWAS ko CEDAO a birnin Accra na kasar Ghana.

Taron dai ya maida hankali ne ga yadda za a kara janyo zuba jarin China a kasashen Afurka, musamman ma a fannonin samar da ababan more rayuwa, da kiwon lafiya, noma da kuma hakar ma'adinai.

Taron ya kuma bada damar musayar ra'ayi tsakani masu ruwa da tsaki akan manufofin kasuwanci na China da kuma Afurka.

Alkaluma dai na nuna cewa, jarin da China ke zubawa a kasashen Afurka zai karu zuwa kashi saba'in cikin dari, wato kimanin dalar Amurka biliyan 50 hamsin.

Yanzu haka dai China na zuba jari a fannoni daban a kasashen Afurka inda take bada dimbin bashi na makudan kudade ga kasashen Afurka domin gina tituna, da asibitoci, da makarantu da kuma gina matatun mai da wuraren hakar ma'adnai.

Wannan yasa a yanzu China ta shiga gaban kowacce kasa a duniya wajen cinikayya da zuba jari a kasashen Afurka.

Cikin 'yan shekarun nan dai tallafin da China take baiwa kasashen Afurka ya zarta wanda sauran manyan kasashe kamar Amurka da Birtaniya da Japan suke bayarwa.

Sai dai kuma wasu kasashen Afurka da ma wasu 'yan Afurkan na ganin huldar kasuwanci tsakanin Afurka da China a matsayin wata barazana.

Masu irin wannan ra'ayi dai na ganin cewa, China ta maida kasashen Afurka tamkar kasuwarsu ta baje koli, inda suke shigo da kaya masu araha dake karya kananan masana'antu a Afurka.

Wasu kuma na korafi ne akan rashin ingancin irin kayan da China ke shigarwa kasuwannin Afurka.

Amma wasu cewa suke, China na tallafawa Afurka ta hanyar ba su bashi ba tare da ruwa ba, kuma ta na soke bashin wasu lokutan.