Mali: 'yan tawaye sun kutsa garin Gao

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kaftin Amadou Sonogo, shugaban mulkin sojan Mali

Azbinawa 'yan tawaye a Mali sun kara dannawa muhimmin garin na Gao dake kudancin kasar. Jami'ai a garin sun ce 'yan tawayen sun shiga garin na Gao ne a cikin motoci kirar a kori-kura shakare da makamai.

An dai bada rahotannin mummunar musayar wuta a garin, kuma hakan yasa shaguna sun rufe, kuma jama'a sun yi ta neman mafaka.

Harin na garin Gao dai ya auku ne kwana guda bayan 'yan tawayen na Azbinawa da hadin gwiwar mayaka masu kishin Islama sun kame garin Kidal.

Ya zuwa yanzu dai mayakan 'yan tawayen Azbinawa da kuma na masu kishin Islama suna tafiya tare, sai dai kuma baa san yadda zasu kasafta ikon da suke samu.

Karin bayani