Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar karancin abinci a yankin Sahel

Image caption Iyalai da dama a Nijer suna fama da yunwa

A yankin Sahel an kiyasta cewa, mutane miliyan 15 da rabi ne yunwa ke yiwa barazana,kusan miliyan 6 da rabi daga cikinsu suna zaune ne a jamhuriyar Nijar.

Abubuwa da yawa ne suka janyo hakan-kamar rashin isasshen ruwan sama, da hauhawar farashin kayayakin abinci, sannan dubban mutanen da suka koma yankin na Sahel sakamakon rikicin Libiya da na Cote d'Ivoire, sun sa matsalar ta dada kamari.

A Nijar kawai kimanin 'yan kasar dubu 200 da 20 ne suka koma gida sakamakon wadannan rikice-rikicen, a daidai lokacin da kasar ke fama da karancin abinci.