BBC navigation

An yi bikin sharar kaburbura a China

An sabunta: 5 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 13:41 GMT

Bikin sharar kaburbura a China

 • Wani mutum yana kunna fitila a wata makabarta a Jinjiang ranar 3 ga watan Afrilun 2012
  Al'ummomi daga China a fadin nahiyar Asiya sun yi bikin shekara-shekara na Qingming, wanda aka fi sani da bikin sharar kaburbura, ranar hudu ga watan Afrilu.
 • Wani mutum yana share kabarin kakanninsa a wata makabarta da ke Taipei, a kasar Taiwan, ranar 4 ga watan Afrilun 2012
  Rana ce wacce mutane ke amfani da ita don tunawa da kakanninsu ta hanayr ziyartar kaburburansu; ana kuma fara bikin ne da share-share na hakika.
 • Wata mata tana tusa rubutun da ke kabarin kakanninta a wata makabarta a Beijing, China, ranar 4 ga watan Afrilun 2012
  A China, da Hong Kong, da ma Taiwan an ba da hutu don tunawa da ranar. A China, ranar 2 ga watan Afrilu aka fara hutun kwana uku.
 • Wasu mutane masu ziyara a kabarin danginsu da ke Shanghai ranar 3 ga watan Afrilun 2012
  Mutane kan gabatar da abinci, da turaren wuta dan tsinke da kuma sauran abubuwan amfanin yau-da-kullum wadanda aka yi da trakarda don amfanin kakanninsu da suka rasu.
 • Yadda ake kona komfiyutar iPad da wayar iPhone na takarda a wata makabarta da ke Fuzhou a kudu maso gabashin China ranar 2 ga watan Afrilun 2012
  A 'yan shekarun nan, abubuwan da ake gabatarwa don amfanin mamata sun karu matuka; daya daga cikin abubuwan da ake batu a kansu bana su ne komfiyutar iPad da wayar iPhone na takarda.
 • Wata mata tana yin addu'a a kabarin wani daga cikin danginta a wata makabarta a Beijing ranar 3 ga watan Afrilun 2012
  Wasu masu fafutukar kare muhalli sun yi magiya ga mutane su rika gabatar da furanni a maimakon haka, saboda kona turaren wuta da takardu yana gurbata yanayi.
 • Wasu masu ziyara a makabartar Babaoshan da ke Beijing yayin bikin Qingming ranar 4 ga watan Afrilun 2012
  Makabartu sun cika sun batse yayin bikin. Rahotanni daga Beijing sun nuna cewa shahararriyar makabartar Babaoshan ta bar kofofinta a bude har zuwa tsakar dare don baiwa mutane damar kai ziyara.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.