Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dambarwar siyasar Mali

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kyaftin Amadou Sanogo

Ranar 22 da watan Maris ne soja karkashin jagorancin Kaptain Amadou Sanogo suka kifar da gwamnatin fara hula ta Mali.

Tun bayan juyin mulkin ne kuma 'yan tawayen Azibinawa suka kame fiye da rabin kasar, ciki har da garin Timbuktu mai dimbin tarihi.

Tuni dai 'yan tawayen suka ayyana 'yancin kai a duk yankunan da suka kame din, kuma hakan ya sake dagula al'amurra a kasar ta Mali.

Sai dai kuma a wani mataki na dawo da doka da oda a kasar ta Mali, kungiyar tarayyar Afrika wato AU da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, sun sanyawa kasar

takunkumin karya tattalin arziki.

Kasashen ECOWAS dake makwabtaka da Malin sun rufe iyokokin su da ita, kuma an hana kasar taba kudadenta dake babban bankin yammacin Afrika.

To wanne irin tasiri wannan matakin matsin lambar zai yi akan sojan dake mulkin kasar ta Mali ? Kuma ko akwai wasu hanyoyin diplomasiyya da za a iya bi don warware wannan matsala ta Mali?