Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsarin koyar da almajirai karatun boko a Najeriya

Image caption 'Yan makarantar allo

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya kaddamar da wani tsarin koyar da almajirai karatun boko da na addini.

Yayin kaddamar da shirin a Jihar Sokoto, Shugaba Jonatahan ya ce, yanzu haka akwai yara miliyan tara da dubu dari biyar wadanda ke yawon bara a garuruwa daban-daban a kasar.

Masana dai na cewa tsarin alamajiranci yana da tsohon tarihi a arewacin kasar ta Najeriya, inda a da can hukumomi ne ke samar da kudaden tafiyar da makarantun daga kudaden Zakkah.

A yanzu dai ana danganta tashi tsayen da gwamnatin Najeriya ta yi domin gina makarantun a matsayin wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar, musanman ma arewacinta.

A karkashin wannan sabon shirin, gwamnatin ta ce za ta gina makarantu dari hudu domin almajirai a jihohi goma sha-tara na arewacin kasar; kuma a cewar gwamnatin, tuni aka kammala gina dari daga cikin makarantun.

Sai dai kuma tuni wadansu suka fara nuna shakku a kan manufar wannan shirin, har ma wadansu malaman makarantun allo na ganin tsarin a matsayin wani shiri ne kawai na hana karatun allo.