BBC navigation

Hatuna: Al'umomi daban-daban na birnin London

An sabunta: 3 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 17:07 GMT

Hatuna: Al'umomi daban-daban na birnin London

 • 'Ya rawa na kasar India
  Wasu 'yan rawa na kasar India na wasa kafin fara rawar gargajiya a wani gidan wasa a London. Akwai 'yan India - wacce Burtaniya da yi wa mulkin mallaka fiye da rabin miliyan a London.
 • Piñata
  Brazil da Colombia sune kasashen da suka fi yawan mutane a London daga Kudancin Amurka. Unguwar Elephant and Castle ta Kudancin London, nan ne 'yan kasar Colombia suka fi yawa.
 • Hoton daurin aure na 'yan Turkiyya
  Arewaci da Kudancin London nan ne matattarar 'yan kasar Turkiyya. Sayar da kayan marmari da abincin Kebab dare-da-rana alama ce ta yadda 'yan Turkiyya ke zaune a wannan yanki.
 • Kantin halal
  A ka'idar addinin Musulunci naman da aka yanka da sunan Allah ne kawai ya halarta a ci. Wannan hoton na nuni da cewa wannan shagon na sayar halartaccen nama ne.
 • Wata mata 'yar kasar Ghana
  'Yan Najeriya da Ghana na daga cikin 'yan Afrika da suka fi yawa a birnin London. Yawancinsu na zaune ne a unguwar Peckham da Hackney. 'Yan Najeriya sun fi yawa a London fiye da ko'ina a duniya banda kasar ta su.
 • Chinatown
  Dandalin Leicester na jan hankalin 'yan yawon bude ido daga ciki da wajen Burtaniya saboda yadda 'yan kasar China suka mamaye yankin. Ana yi masa lakabi da birnin China.
 • Shagunan kayan kawa a Brixton
  Yankin Brixton na daga cikin yankunan da ya fi tara al'umma iri daban-daban. 'Yan kasar West Indies ne suka fi yawa a wannan yanki. Sana'ar da aka fi yi a yankin ita ce ta sayar da kayan kawa - yadda mata za su iya sauya fasalinsu.
 • Unguwar Yahudawa
  Yankin Stanford Hill na Arewacin London kuwa, gida ne ga Yahudawa daga Gabashin Turai. Suna zaune a gefe ba tare da sauran jama'ar gari ba, inda suke gudanar da al'adunsu na gargajiya.
 • Matan Musulmi
  Wurin shakatawa na London, musamman Hyde Park da Regent's Park nan ne wurin ganawa da haduwa na al'ummar Musulmi a London. Musulunci ya hana su shiga mashaya, don haka nan ne wuraren da suke tarurrukansu.
 • Al'umar kasar Bengladesh
  Al'umar kasar Bengladesh su ne suka fi karanci amma kuma suna bunkasa cikin gaggawa a birnin na London. Suna zaune ne a Gabashin birnin inda suke sayar da kazar Tikka masala da kuma tufafi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.