BBC navigation

Matan Ghana masu tashi sama

An sabunta: 16 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 18:01 GMT

Matan Ghana masu tashi sama

 • Patricia Mawuli
  Patricia Mawuli kwararriyar mai tukin jirgi ce har da takardar shaida, injiniyar jirgin sama, kuma 'yar Afirka guda daya tilo da ta cancanci hada injinan Rotax wadanda ake amfani da su a kananan jiragen sama. Yanzu haka tana taimakawa wajen gudanar da Makarantar Koyan Tukin Jirgi ta Ghana, wato Aviation and Technology Academy (AvTech), mai nisan kilomita 50 a arewa maso gabashin birnin Accra.
 • Filin jirgin sama na Kpong a Ghana
  Makarantar a Kpong take, daya daga cikin filayen jiragen sama masu zaman kansu inda aka fi hadahada a Afirka ta Yamma. Akan yi hayar jiragen AvTech saboda wasu aikace-aikace kamar feshin maganin kwari a gonaki, daukar hoto ta sama, da kuma rarraba kayan agaji. Ana kuma bayar da kebantattun darussan tukin jirgi ga masu sha'awa: kudin da ake samu daga koyarwar ne ma ake amfani da su don baiwa 'yan mata da matan yankin horo.
 • 'Yanmatan Ghana suna gyara injin din jirgi
  Dan Burtaniya Jonathan Porter ne ya mallaki AvTech. Shi injiniya ne kuma malamin tukin jirgin sama. Mutanen yankin sun fi sanin shi da suna "Captain Yaw". Lokacin da ya koma Ghana ya tafi da dan karamin jirginsa da burin yin amfani da shi don inganta rayuwar matalauta a yankunan karkara.
 • Lydia Wetsi, mai nakasa, da Juliet Kruuwa suna wasa kwakwalwa bayan sun tashi daga makaranta
  Ana koyawa Lydia Wetsi da Juliet Kruuwa, biyu daga cikin daliban AvTech, dukkan abin da suke bukatar sani dangane da kananan jiragen sama--kama daga hada su zuwa tuka su. Da zarar sun kammala karatunsu na shekaru hudu kuma za su samu takardar shaidar da aka yarda da ita a fadin duniya.
 • Lydia Wetsi tana gyara injin din rotax wanda ake amfani da shi a kananan jiragen sama
  A da burin Lydia Wetsi, wacce ba ta iya amfani da hannunta na dama tun da aka haife ta, shi ne ta zama mai gyaran gashi. Ta sauya ra'ayi ne lokacin da ta samu damar shiga jirgin sama. Yanzu burinta shi ne ta zama mai tukin jirgin sama ta kuma rika zuwa yankunan karkara a jirgin don koyar da al'umma yadda ake kula da lafiyar yara. Nan da shekaru biyu za ta samu bajen tukin jirgi.
 • Patricia Mawuli tana dudduba jirginta kafin ta tashi
  Tun tana yarinya jiragen sama ke burge Patricia Mawuli. A lokacin ta kan ga jirage na wucewa ta Tafkin Volta, tafki mafi girma da mutum ya tona a Afirka, inda mahaifinta ke kamun kifi; ta kan daga murya tana ba su sako su kawowa iyalinta abubuwa.
 • Daya daga cikin titunan jirgin sama na filin jiragen sama na Kpong daura da tsaunukan Shai a gabashin Ghana
  Shekaru biyar da suka wuce Mis Mawuli ta yi aiki a wannan filin, inda ta taimaka wajen cire kututturen bishiya don samar da titunan jiragen sama na Kpong guda biyu. Saboda yadda kasancewarta kusa da jiragen saman da take ta gani ta ba ta sha'awa, sai ta roki "Captain Yaw" ya koya mata tukin jirgi.
 • Juliet Kruuwa tana dudduba daya daga cikin kananan jiragen saman
  Makarantar AvTech kan baiwa dalibai kudin kashewa yayin da suke horo; idan suka kammala kuma suna da tabbacin samun aiki, ko dai a garejin makarantar, ko kuma a kamfanonin da ke da alaka da ita.
 • Hasumiyar kula da tashi da saukar jirage a filin jirgin sama na Kpong
  'Yanmata da matan AvTech masu tashi kalluba ne a tsakanin rawuna a Ghana, kasar da mata matuka jirgin sama kalilan ne, sannan kuma su suna da kwarewar hadawa da kuma kula da jiragensu. (Sammy Darko ne ya dauko wadannan hotunan)

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.