Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar tsaro a Najeriya, Ina Mafita..?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu motocin da aka kaiwa hari a wani Coci

Matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu birane musamman a arewacin Nijeriya. Wannan lamari dai na haddasa asarar rayuka da jikkata jama'a da mada a kasar.

Ranar Lahadin da ta wuce ne dai aka wayi gari da tashin bamabamai a wasu mujami'u a biranen Zaria da Kaduna cikin jihar Kaduna. Wannan lamari ya haddasa asarar rayuka da jikata jama'a.

Hakanan ma rikicin da ya biyo bayan tashin bamabaman sun haddasa karin mace macen jama'a da jikata wasu da kuma salwantar dukiya mai dimbin yawa. Yanzu haka dai dokar hana fita ba dare ba rana na aiki a jihar ta Kaduna ko da yake an dan sassautata a ranakun yau juma'a da kuma Lahadi domin ba jama'a damar yin ibada.