Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Fiye da mutane 100 sun mutu a Najeriya

Fiye da mutane dari ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wata tankar daukar mai tayi taho mu gama da wata bas a jihar River dake yankin Niger Delta a Najeriya. Hukumomi sun ce, an yi asarar wadannan rayuka ne yayin da jama'a suka shiga kalen man fetur din da tankar ta zubar, inda kuma hakan ya haddasa gobara, wadda ta koma mutane da dama kurmus.