Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Menene ya sa aka kasa shawo kan talauci?

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Yawan matalauta a duniya ya ragu da rabi

Magance talauci dai na cikin batutuwan da Majalisar Dinkin Duniya ta saka a cikin muradun wannan karnin, wadanda ta ce za ta yi kokarinkawar da su a tsakanin al'ummomin duniya daga nan zuwa shekara ta 2015.

Sai dai kuma yayin da wadansu kasashe ke ci gaba da yin hobbasa don ganin cewa sun rage yawan matalauta, wata cibiyar kwararru mai nazari a kan ci gaban kasa-da-kasa, wato Overseas Development Institute da ke Birtaniya, ta bayyana cewa talauci ya ragu ta rabi cikin kusan shekaru ashirin da biyu da suka wuce.

Amma kuma a cewar rahoton kwararrun, wadansu kasashe wadanda al'umominsu ke kara yawaita har yanzu talaucin na nan yadda yake tun shekarar 1990.

Ita dai cibiyar ta ce daya daga cikin hanyoyin magance wannan matsalar ta talauci ita ce masu hannu da shuni su rika bayar da taimako ga talakawa musamman a kasashe matalauta.