Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tawagar Olympics ta Somalia ta isa London

A ci gaba da shirye-shiryen gasar Olympics, tawagar 'yan wasan Somalia ta isa birnin London, inda suka zamo 'yan kasar na farko da suka samu izinin shiga Burtaniya kai tsaye daga kasar ta Somalia a cikin shekaru 20. Sun isa filin saukar jiragen sama na Heathrow ne akan idon Naziru Mikailu, ga kuma rahoton da ya aiko mana.