BBC navigation

Hotuna: Wuraren da za a yi wasannin Olympic a Landan

An sabunta: 27 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 18:36 GMT

Hotuna: Wuraren da za a yi wasannin Olympic a Landan

 • Filayen wasannin Olympics
  Kasaitaccen filin wasa na Olympics na yin maraba ga mutanen da ke wuce wa ta kofar shiga filin ajiye motoci da ke Stratford, a gabashin London. Filin wasan na da kujerun wucin gadi wadanda za a iya cire wa da zarar an kammala gasar. Hoto Jason Hawkes
 • Filayen wasannin Olympics
  Wannan bangaren wanda wani mai zane dan kasar Iraqi Zaha Hadid ya zana, anan ne za a gudanar da wasannin ninkaya, za a cire kujerun da zarar an kammala gasar a 2012. Duka hotunan na kamfanin Getty / London 2012 sai wadanda aka fayyace.
 • Filayen wasannin Olympics
  Wannan bangaren da za a gudanar da wasan kwallon kwando na daya daga cikin filaye mafiya girma da aka gabatar da wasannin Olympics. Mutane 12,000 za su iya haduwa a wannan filin. Kuma za a iya gudanar da wasannin Olympic da na nakasassu da ake kira 'Paralympic', filin zai kuma karbi bakuncin wasan kwallon kwando.
 • Filayen wasannin Olympics
  Filin ajiye motoci na Velodrome ne aka fara kammalawa a watan Fabrerun 2011. An nemi shawarar tsohon zakaran wasan Olympics Sir Chris Hoy wurin zana filin sannan kuma ya yaba da yadda filin ya kasance. Kofa ta gaba ita ce ta BMX.
 • Filayen wasannin Olympics
  Filin wasa na kwallon Hockey an gina shi ne a matsayin na wucin gadi a Arewa maso Yammacin filin Olympic. An gina shi ne ta yadda zai baiwa jama'a damar kallon wasa daga filin da kuma London. Za kuma ayi amfani da filin wajen wasan kwallon kafa na nakasassu. Hoto - Populous
 • Filayen wasannin Olympics
  Filin wasan kwallon hannu shi ne ya karbi bakuncin wasan gwajin da aka yi a shekara ta 2011. An kawata kujerun filin da farin fenti, inda yawancinsu suke a zagaye. Filin ne kuma zai karbi bakuncin wasan pentathlon na Olympics da kuma goalball a wasan nakasassu.
 • Filayen wasannin Olympics
  Yawancin wasannin za a gudanar da su ne a wajen filin wasa na Olympic Park a kewayen London. Hyde Park da ke tsakiyar birnin zai karbi bakuncin triathlon yayin da za a gudanar da wasan ninkaya a Serpentine. Sauran wasannin ninkayarma a nan ne za a gudanar da su.
 • Filayen wasannin Olympics
  Za a gudanar da wasan kwallon raga ta yashi a Horse Guards Parade. Masu shirya gasar ta London 2012 sun ce kafa filayen wasa na wucin gadi a sassan birnin London, zai fito da yadda London za ta kasance cibiyar wasan. Hoto - PA
 • Filayen wasannin Olympics
  Za a yi wasu wasannin a filin gasar kruket, filin da ke da cibiyar watsa labarai. Wadanda za su fafata a gasar za su yi tafiya a wani waje na musamman ba wai inda aka saba bi ba har zuwa karshen gasar ta Olympics. Hoto - Populous
 • Filayen wasannin Olympics
  Wurin tarihi na Greenwich Park a Kudu maso gabashin London zai dauki bakuncin wasu wasanni da suka hada da pentathlon. Za a gudanar da sauran wasannin da suka hada da na tsalle-tsalle a gaban gidan Sarauniya wanda aka gina a karni na 17. Hoto - Populous
 • Filayen wasannin Olympics
  Tashar jiragen ruwa ta London da ke Woolwich na da tarihi na soji da kuma gini na barikin sojojin fannin atilari tun a shekarar 1776 inda aka yi gasar Olympic a wajen.
 • Filayen wasannin Olympics
  A daya bangaren birnin, fadar sarki Henry na takwas da ke yankin Hampton ta nan ne ake farawa da kamalla tseren keke na Olympics, a yayin da sauran yankin na kudu maso yammacin London ake sauran tseren na Olympics.
 • Filayen wasannin Olympics
  Wajen tennis mai tarihi d ake kira All England Club da ke Wimbledon na daga cikin wajen da za a yi gasar Olympics daga ranar 28 ga watan Yuli zuwa biyar ga watan Agusta.
 • Filayen wasannin Olympics
  Daga hagu: Filin wasa na Wembley zai dauki bakuncin gasar kwallon kafa a yayin da a Wembley Arena za a yi wasannin badminton da rhythmic gymnastics, Excel - boxing, fencing, judo, table tennis, taekwondo, weightlifting da kuma dambe; sai filin North Greenwich Arena - inda za a yi gymnastics, trampoline da kwallon kwando.
 • Filayen wasannin Olympics
  Wurare a wajen London na daga cikin inda za a yi gasar Olympics. Kamar tsibirin Dorney wanda za a yi wasanni na musamman a shekara ta 2012. Sannan kuma za a yi horo na wasu wasannin ninkaya.
 • Filayen wasannin Olympics
  Tashar jiragen ruwa ta London da ke Woolwich na da tarihi na soji da kuma gini na barikin sojojin fannin atilari tun a shekarar 1776 inda aka yi gasar Olympic a wajen.
 • Filayen wasannin Olympics
  Zaratan wasan hawan tsauni za su fafata a gonar Hadleigh da ke Essex a lokacin gasar ta 2012. Za a yi amfani da wajen sosai a gasar.
 • Filayen wasannin Olympics
  Cibiyar Lee Valley White Water da ke Hertfordshire nan ne waje na farko da aka kammala don gasar Olympics tun a watan Disambar 2010. Masu tseren jirgin ruwa su ne za su kasance a wajen. Sai kuma wasu masu tseren da za su yi a Weymouth da Portland da ke Dorset, inda anan za a ga wajen tarihi a Burtaniya. Kuma a halin yanzu ana ci gaba da bunkasa wajen.
 • Filayen wasannin Olympics
  Za a soma gasar London 2012 a Cardiff da kwallon kafa na mata a ranar 25 ga watan Yuli wato kwanaki biyu kafin bukin bude gasar. Za a yi amfani da filayen kwallon kafa a Burtaniya lokacin gasar. Daga hagu: Hampden Park, Glasgow; St James' Park, Newcastle; City of Coventry Stadium; Wembley, London; Millennium Stadium, Cardiff and Old Trafford, Manchester.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.