BBC navigation

Nasarorin Usain Bolt cikin hotuna

An sabunta: 6 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:51 GMT

Nasarorin Usain Bolt cikin hotuna

 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Usain Bolt ya fara fafatawa a fagen duniya ne a shekara ta 2004, amma bai fara haskakawa ba sakamakon raunin da ya samu a gasar tseren duniya ta 2005 a birnin Helsinki
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Bolt na yin atisayi sosai domin murmurewa, inda ya shafe lokacinsa a jami'ar West Indies
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Sai dai ya halarci gasar kasashen Commonwealth ta 2006 a Melbourne ba, saboda rauni, amma ya ja hankalin duniya a watan Mayun 2008 lokacin da ya kafa tarihi a tseren mita 100 a New York a dakika 9.72
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Ya halarci gasar Olympics ta 2008 a Beijing, inda ya lashe tseren mita 100, ya fara murna tun kafin ya tsallake layin karshe.
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Bolt ya samu nasara ne a dakika 9.69, fiye da dakikar da yayi nasara da ita a baya
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Sabon zakaran mita 100 na duniya ya kara samun daukaka ta hanyar kirkiro da yadda yake murna kan nasararsa
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Yana cikin wadanda ake ganin za su samu nasara a World Championships a Daegu a 2011, amma sai ya gamu da cikas bayan ya fara wasan ba bisa ka'ida ba.
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Bolt ya yi takaici bayanda aka kore shi daga wasan karshe abinda ya baiwa abokin karawarsa na Jamaica Yohan Blake damar zamowa zakaran duniya
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Yohan Blake ya doke Bolt a wasan share fagen Olympics na Jamaica a 2012
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Yana kokarin nishadantar da mutane duk inda ya je, kamar yadda yake tsere da Yarima Harry kafin fara gasar Olympics
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Tun kafin fara gasar Olympics ta 2012, masu shirya gasar sun san wanda zai fi jan hankalin jama'a
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Koda aka shiga fili a wasan karshe na mita 100 a London, ana nuna shakku kan ko Bolt zai iya kai labari ganin yadda aka yi nasara a kansa a wasan share fage
 • Usain Bolt - The Olympic 100m champion in pictures
  Amma sai ya rufe bakin masu shakka inda ya yi nasara cikin sauki a dakika 9.63 tare da kafa sabon tarihi a gasar Olympics

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.