Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amsoshin Takardunku: Asalin tashe a kasar Hausa

Hakkin mallakar hoto Reuetrs
Image caption Musulmi na buda baki a masallaci a lokacin azumi

Wasan tashe wata al'ada ce da ake yi a kasar Hausa a lokacin azumin watan Ramalana, inda matasa har ma da yara kan yi shiga kala-kala, suna kida da waka.

Tashe hanya ce ta fadakarwa, ilmantarwa da kuma ankarar ko nusar da mutane game da wasu batutuwan da suka shafi rayuwa.

Sannan ana amfani da tashe wajen tashin mutane daga barci domin su dauki sahur.

Kuma a kan sallami masu tashe da kudi, hatsi da dai sauransu.

Haka kuma tashe hanya ce ta nishadantar da masu azumi don su manta da gajiyar da suke tare da ita.

To menene asalin wasan tashe a kasar Hausa.

Mallam Tijjani Shehu Almajir ya bayyana asalin tashe a kasar Hausa.