Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Ko me ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a Olympics

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tutar Olympics mai alamar zobba

An kammala gasar wasannin Olympics ta shekarar 2012 a London, amma kasashen nahiyar Afrika da dama ba su tabuka wani abin a zo a gani ba.

Kasashe kamar su Najeriya na ci gaba da yin nazari a kan dalilan da suka janyo musu rashin samun lambar yabo a gasar.

Kuma a cewar mukaddashin shugaban tawagar Najeriya a gasar Olympics, Alhaji Alhassan Yakmut, yakamata kasar ta farka daga barcin da take yi.