Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Ko yaya Sallar bana za ta same ku?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masallacin Kudus

A karshen wannan makon ne ake sa ran al'ummar musulmi a fadin duniya zasu yi bukukuwan Sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadhan.

Al'ummar musulmi dai sun kwashe tsawon wata guda suna azumin watan Ramadhan wanda daya ne daga cikin shika-shikan musulunci.

A watan na Ramadan dai musulmi kan yawaita ibada, karanta Al Qur'ani mai tsarki da kuma taimakawa tallakawa masu karamin karfi.

Kafin dai bukukuwan Sallar akan bada zakkar fidda kai, kuma ranar Sallar akan je masallaci domin yin Sallar Idi.

Sallah dai lokaci ne na nuna farin ciki da kuma sada zumunci ga duk al'ummar musulmi.

Sai dai kuma a sassa daban daban na duniya sallar kan zo ga musulmi cikin yanayi iri daban-daban, inda wasu ma ka iya cewa, bara ta fi bana, ko kuma wasu su ce bana ta fi bara.