BBC navigation

Ra'ayi Riga:Ko yaya Sallar bana za ta same ku?

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:48 GMT

Garmaho

A karshen wannan makon ne al'ummar musulmi a fadin duniya zasu yi bukukuwan Sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadhan.Azumin Ramadhan daya ne daga cikin shika-shikan musulunci.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

aqsa

Masallacin Kudus

A karshen wannan makon ne ake sa ran al'ummar musulmi a fadin duniya zasu yi bukukuwan Sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadhan.

Al'ummar musulmi dai sun kwashe tsawon wata guda suna azumin watan Ramadhan wanda daya ne daga cikin shika-shikan musulunci.

A watan na Ramadan dai musulmi kan yawaita ibada, karanta Al Qur'ani mai tsarki da kuma taimakawa tallakawa masu karamin karfi.

Kafin dai bukukuwan Sallar akan bada zakkar fidda kai, kuma ranar Sallar akan je masallaci domin yin Sallar Idi.

Sallah dai lokaci ne na nuna farin ciki da kuma sada zumunci ga duk al'ummar musulmi.

Sai dai kuma a sassa daban daban na duniya sallar kan zo ga musulmi cikin yanayi iri daban-daban, inda wasu ma ka iya cewa, bara ta fi bana, ko kuma wasu su ce bana ta fi bara.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.