BBC navigation

'Yan wasan kwallon Afirka a Gasar Premier

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:59 GMT

'Yan wasan kwallon Afirka a Gasar Premier

 • Dan wasan tsakiya na Ivory Coast, Yaya Toure (a shudiyar riga), zai sake zama zakaran gwajin dafi a Manchester City a yunkurinsu na sake lashe Gasar Premier. Kasancewar Yaya a kungiyar ta Manchester City ta taka muhimmiyar rawa a kakar bara, sannan kuma ya jefa kwallaye masu zafi a raga - ga alama kuma za a ci gaba da ganin hakan idan aka yi la'akari da rawar da ya taka a nasarar da suka yi a kan Chelsea da ci uku da biyu a wasan cin Garkuwar Community Shield.
 • Hakazalika Manchester City din na da dan wasa mai tashe, wato Abdul Razak (a shudiyar riga), wanda karansa zai iya kai tsaiko mamaki bana. Tuni dan wasan na tsakiya mai shekaru 19 da haihuwa ya samu gurbi a tawagar Ivory Coast kuma zai zaku ya ya ci gaba da takawa City leda bayan ya kuskurewa fitowa a wasan cin Garkuwar Community Shield.
 • Wigan ta samo dan wasan gaba na Ivory Coast Arouna Kone (a gefen hagu) wanda ya ce saboda falsafar kwallo ta kocin Wigan Roberto Martinez da salon wasanta ya shiga kungiyar. Kone, dan shekara 28, ya koma Wigan ne daga kungiyar Levante ta Spain, inda ya ci kwallaye 15 a wasanni 34 a kakar wasanni ta bara.
 • Sai dai kuma kungiyar ta Wigan ta yi asarar mai tsaron baya na Senegal Mohamed Diame, wanda ya koma kungiyar West Ham. Kungiyar ta birnin London za ta yi fatan dan wasan zai taimaka mata ta zauna a Gasar Premier wadda a kakar bana ta shiga.
 • Haka nan kuma kungiyar ta Wigan ta dauko wani hazikin da wasan Afirka, wato Modibo Maiga, wanda ke bugawa tawagar Mali wasan gaba ko na gefe. Ya dawo kungiyar ta gabashin London ne daga Sochaux. Saboda matsuwar da ya yi ya bar fagen gasar Faransa har yajin aiki ya yi a kakar wasa ta bara don tilastawa kungiyar ta kyale shi ya tafi Newcastle.
 • Victor Moses ma (a gefen dama) wani tauraron dan wsa ne na Afirka a Gasar Premier, ko da yake har yanzu ba shi da tabbas a kan Wigan zai takawa leda ko Chelsea, kungiyar da ke kokarin sayen shi daga Latics. Dan wasan mai dan karen gudu ya bugawa Ingila a matakin 'yan kasa da shekaru 21 amma ya zabi bugawa Najeriya a matakin manya, kuma sau uku yana takawa Super Eagles leda.
 • A watan Janairu Papis Cisse ya shiga sahun 'yan wasan Newcastle kuma dan wasan na Senegal bai bata lokaci ba ya zama dan gida, har ma ya ci kwallaye 13 a wasanni 14. A kakar wasa ta bara kungiyar ta Newcastle ta kare ne a matsayi na shida a teburin Premier kuma za ta bukaci Cisse ya yi wuta kamar bara in har tana so ta kwata hakan.
 • Kashin bayan wasan gaban Newcastle tagwayen masu ne wadanda suka fito daga Senegal. Baya ga Papis Cisse, dayan shi ne Demba Ba. Wannan kakar wasa ce ta biyu da Ba zai taka leda ga kungiyar ta Newcastle kuma zai yi burin inganta nasarar da ya yi bara ta cin kwallaye 16.
 • Nan ba da jimawa ba karfin kungiyar Liverpool zai karu da zuwan Oussama Assaidi, dan wasan Morocco mai shekaru 24, wanda ke dab da komawa kungiyar daga Heerenveen ta kasar Holland. Assaidi ya takaw kasarsa wasanni har 22 kuma ya ci wa Heerenveen kwallaye 20 a wasanni 68.
 • An zabi dan wasan Jamhuriyar Benin Stephane Sessegnon a matsayin gwarzon dan wasa na Sunderland a kakar wasa ta bara, wadda kuma ita ce kakarsa ta farko a kungiyar. Dan wasan mai shekaru 28 ya buga wasanni 42 ya kuma ci kwallaye 10.
 • Kakar wasa ta bara ce ta fi kowacce ga Alex Song a Arsenal, lokacin da ya dauki hankalin 'yan kallo da yadda yake gyara kwallo da kuma zalakarsa ta tsaron baya. Sai dai nan ba da jimawa ba dan wasan na Kamaru zai bar Gasar Premier ya koma ta La Liga-- Barcelona ta nuna sha'awar sayen dan wasan mai shekaru 24.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.