BBC navigation

Habasha na alhinin Firai minista Zenawi

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 14:03 GMT

Labarai Cikin Hotuna: Gawar Firai Ministan Habasha Meles Zenawi

  • Mutane sun yi dafifi a Adis Ababa dauke da hotunan Firai Minista Meles Zenawi, a yayin da suke jiran isowar gawarsa.
  • Dubban 'yan Habasha sun taru a babban birnin kasar wato Adis Ababa a ranar Talata don nuna alhininsu ga mutuwar Zenawi.
  • Wannan jirgin ne ya kawo gawar Firai Ministan Meles Zenawi Adis Ababa da sanyin safiyar ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2012.
  • An ajiye gawar Mr. Meles a fadar kasar dake Adis Ababa don mutane su yi mata kallon karshe.
  • Meles ya yi kane-kane a harkar siyasar Habasha fiye da shekaru ashirin.
  • Ana raka gawar Firai ministan a cikin wannan bakar motar.
  • An kunna kendir a kusa da hoton tsohon Firai Ministan Habasha, Meles Zenawi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.