Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Samar da rundunar 'yan sanda a Jihohin Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya

Batun kafa rundunar 'yan sanda mallakar jihohi a Najeriya , za a iya cewa shine abin da ya kankane mahawarar da ake yi a fagen siyasar kasar.

Yanzu haka wasu 'yan kasar na ganin cewa lokaci yayi da za a samu 'yan sanda karkashin ikon jihohin kasar, don taimakawa rundunar 'yan sandan dake karkashin ikon gwamnatin tarayya.

Tsafaffin speto janar na 'yan sanda kasar na rukunin wadanda ba sa son a kirkiro rundunonin 'yan sanda karkashin jihohi, saboda yiwuwar gwamnonin su yi amfani da 'yan sandan a matsayin karnukan farautarsu.

Ita kuwa kungiyar lauyoyin kasar wato NBA gani take cewa lokaci yayi da kasar za ta samu 'yan sandan jihohi.

Shima tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Ibrahim Badamasi Babangida an ambato shi yana nuna goyon bayansa game da shirin kirkiro rundunar 'yan sandan ta jihohi.

To ko menene kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar game da haka?

Shin ta yaya za a tabbatar da adalci tsakanin mutane biyu wadanda suka samu rashin fahimtar juna a inda ake kallon daya daga cikinsu dan asalin jihar ne , dayan kuma ake masa kallon bako?

Wadannan na daga cikin tambayoyin da shirin Ra'ayi riga na wannan makon ya duba.