BBC navigation

Bikin bude gasar wasanni ta nakasassu

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 11:38 GMT

Bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu

 • Wasan wuta ya haskaka sararin samaniya
  Sarauniyar Ingila, Elizabeth ce ta bude gasar da ake yi a London a shekarar 2012, a wani kasaitaccen bikin da ya samu halartar 'yan kallo dubu 80.
 • Kwamandan, Joe Townsend dauke da wutar gasar Paralympics
  Kwamandan jiragen ruwa na Birtaniya Joe Townsend na cikin wadanda za su fafata a gasar, bayan ya rasa kafafuwansa a yakin Afghanistan. An zuro shi ne cikin filin wasan da wata waya daga saman husumiyya ta Orbit.
 • Margaret Maughan ta kunna wutar Paralympics
  Mr. Townsend ya mika wutar ga Margaret Maughan, wacce ta samu lambar zinare a wasan harbin kibau a gasar nakasassun da aka yi a birnin Roma a shekarar 1960. Inda ta kunna wata 'yar wuta a kasa, sai wuta fiye da 200 da aka tsara kamar fure ya kama. Sannan suka zama tukunyar wuta, wata alama ta hadin kai.
 • 'Yar wasan ninkaya ta Jamus, Daniela Schulte
  Tawagogi daga kasashe 165 suna fareti a filin wasan a wani bangare na bikin da wadanda suka shirya shi suka sa wa suna Spirit in Motion.
 • An daga tutar gasar nakasassu ta Paralympics
  Mambobin tawagar Birtaniya da za su fafata a gasar kwallon kwando na 'yan kasa da shekaru 22 su takwas sun shiga filin wasan dauke da tutar gasar Paralympics wadda dakarun soji suka daga sama.
 • Jirgi ya bi ta saman filin wasan a lokacin bude gasar
  Jirgin sama mai aman wasan wuta ne ya bude gasar. Jirgin dai na kungiyar jin kai ta Birtaniya ce, Aerobility dake horar da nakasassu wajen koyon tukin jiragen sama.
 • Farfesa Stephen Hawking
  Farfesa Stephen Hawking ne ya bude gasar, inda ya yi jawabi a kan bukatar fahimtar duniya. Masu shirya gasar dai sun ce bikin ya ta'allaka ne kan kimiyya da kuma bil'adama.
 • Bikin dube gasar Paralymics ta London a shekarar 2012
  Wani haske mai karfin gaske dake harbawa sama kuma ya sauko a tsakiyar filin kewaye da wata katuwar lema.
 • 'Yar wasa Nicola Miles-Wildin
  A daukacin lokacin bikin, Farfesa Hawking ya kasance dan jagora ga Miranda wata tauraruwar 'yar wasan Wiilam Shakespeare, wadda 'yar wasa Nicola Miles-Wildin ke kwaikwayo.
 • Masu rawa sun bude lema a gurin bikin
  Kimanin masu sa kai dubu uku ne suka shiga bikin bude gasar. An hada wutar ko ta kwana a dakin taro na City don tabbatar da an fara bikin a kan lokaci bayan jinkirin da aka samu.
 • Mutum-mutumin Marc Quinn
  An sake yin mutum-mutumin Marc Quinn, Alison Lapper mai ciki da aka kwaikwaya daga wani dandamali da aka yi wa tsarin littafin.
 • Yarima Edward, Earl na Wessex, Sophie
  Shugaban kwamitin shirya gasar nakasassu na kasa da kasa, Sir Philip Craven ne ya tarbo Sarauniyar Ingila. Kuma wannan ne karon farko da ta bude gasar wasanni biyu na Olympics da kuma ta Paralympics.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.