Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Jirgin Afrika Express ya kama hanya

Jirgin Africa Express dauke da mawaka kusan 80 daga Afrika, Turai da sauran sassan duniya, ya soma balaguron mako guda domin kewaye Burtaniya, a wani bangare na murnar gasar wasannin Olympic da Paralympic. Mawaka da suka hada da Afel Bocoum, Amadou & Mariam, Bassekou Kouyate, Baaba Mal, Rokia Traoré, Tony Allen da Toumani Diabate, na cikin wadanda ke wannan balaguro.