BBC navigation

Jirgin Africa Express cikin hotuna

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:48 GMT

Jirgin Africa Express cikin hotuna

 • Amadou da Romeo Stodart
  Jirgin Africa Express, wani jirgi dauke da muhimman mawaka tamanin daga nahiyar Afrika da Turai da kuma sauran sassan duniya. Suna kewayawa yankuna daban-daban na kasar Burtaniya har tsawon mako guda. A nan ana iya ganin masu kada jita amadou Bagayoko daga kasar Mali da kuma Romeo Stodart daga tawagar mawakan Magic Numbers na Burtaniya. Manuel Toledo na sashen Africa na BBC ne ya dauko mana hotunan.
 • Jirgin Africa Express ya isa garin Stoke-on-Trent
  Kewayen na daga cikin wani shiri da aka fara shi a shekarar 2006 lokacin da mawakan Rock na Burtaniya Damon Albarn da Gorilaz fame da kuma mai shirya waka Stephen Budd da dan jarida Ian Birell suka hada gwuiwa domin watsa wake-wake nahiyar Afrika ga masu saurare a sassan duniya da dama.
 • Mawaka da ke tafiya a jirgin Africa Express
  Wasu daga cikin manyan mawaka daga Afrika da suka hadar da Baaba Mal, Rokia Traore, Tony Allen da kuma Bassekou Koyate na daga cikin mawakan da ke tafiya a jirgin. A nan sun hadu ne da wasu matsan mawaka.
 • Damon Albarn ya hadu da mawakan Rap Rap Reeps One, African Boy, M.anifest, Pauli The PSM, tare kuma da Hama Sangare
  Mawakan da ke cikin jirgin na hadin kai da junan su, suna ta raha tsakaninsu. A nan za a iya ganin Damon Albarn na waka tare da mawakan Rap Reeps One, African Boy, M.anifest, Pauli The PSM, tare kuma da Hama Sangare suna kidan kwarya da waka.
 • Tony Allen
  Kwararren mai kidan gangar nan na Najeriya Tony Allen ya samu gagarumin yabo da tafi. Ya shahara a Burtaniya ta hanyar alakarsa da mawaki Fela Kuti, wanda tare suka kirkiro da wakar nan samfurin Afrobeat, sannan kuma sun nadi wakoki tare da Albarn.
 • Baaba Maal
  Kewayen na Africa Express a Burtaniya wani bangare ne na bukukuwan da ake gudanarwa na London 2012, kuma suna gudana ne kafada da kafada da gasar Olympics da Paralympics. mawakin kasar Senegal Baaba Maal shi ne daraktan tsara al'adu na Africa Utopia, wani bikin na daban da akan shafe wata guda ana gudanarwa kan al'adun nahiyar Africa a cibiyar South Bank da ke London.
 • Mawaki kuma mai kada violin Marques Toliver dan Amurka ne tare da dan Senegal Massamba Diop a tasahar jirgin kasa ta Stoke-on-Trend
  A wasu lokutan jirgin yakan tsaya kuma mawaka su yi ta kade-kade da raye-raye a kan dandamalin tashohin jiragen kasar, hakan kuma na baiwa masu kallo da dama mamaki. A nan mawaki kuma mai kada violin Marques Toliver dan Amurka ne tare da dan Senegal Massamba Diop ke kayatar da jama'a a tashar jirgin kasa ta Stoke-on-Trend.
 • Mawakan Jupiter and Okwess International
  Ana kuma jin kade kaden kasar Congo a wurare da dama da jirgin ya tsaya. Mawakan Jupiter and Okwess International da ke Kinshasha ne ke kayatar da jama'a.
 • Rokia Traore da Romeo Stodart da Mamah Diabate da Diabel Cissokho da M.anifest na wasa a wajen nadar Leeds' Jumbo.
  Kowacce rana mawakan sukan leka makarantu, cibiyoyin al'umma, wuraren adana kayan al'adu da sauransu. A nan Rokia Traore da Romeo Stodart da Mamah Diabatem da Diabel Cissokho da M.anifest ne ke wasa a wajen nadar wakoki na Leeds' Jumbo.
 • Spoek Mathambo da Kareem Rush da M1
  Daga wani bangaren Afrika zuwa wani, a nan mawakin Rap na kasar Afrika ta Kudu Spoek Mathambo da ke kusa da taga na tare da mawaki dan kasar Masar Kareem Rush na kungiyar mawakan Arabian Knightz, da kuma mawaki M1 na kungiyar mawakan hip hop na Amurka Dead Prez.
 • Harley "Sylvester" Alexander-Sule tare da magoya bayansu
  Mawakan hip hop na Rizzle Kicks na jan hankalin magoya bayansu. Harley "Sylvester" Alexander-Sule, a wannan hotono, da Jordan "Rizzle" Stephen, sun shaida wa BBC cewa bayan kammala wannan balaguron za su ci gaba da hada kai da mawakan Afrika.
 • Middlesbrough
  Kawo yanzu mawakan Afrika sun gudanar da wakoki a biranen Middlesbrough, Glasgow, Manchester da kuma Cardiff. A wannan hoton akwai Mim Suleiman na Tanzania, Malian ngoni player Bassekou Kouyate, violinist Marques Toliver da kuma Kyla La Grange.
 • Express Horns na gwajin wakokin da za su yi. A bayansu akwai Ian Birrell, ta hagu kuma akwai Stephen Budd da Damon Albarn na Africa Express.
 • Mawaka na isa birnin Glasgow
  Mawakan sun samu kyakkyawar tarba a birnin Glasgow na Scotland. Daga bisani 'yan wasan bagpipe sun hadu da Jupiter & Okwess domin yin waka tare.
 • Mawaka na wake-wake a cikin jirgi
  Za a ci gaba da wannan balaguro a 'yan kwanaki masu zuwa. Inda za a gudanar da wasanni a Bristol da kuma London - inda anan ne za a kammala wannan tafiya mai cike da tarihi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.