Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Najeriya ta taka rawar gani a gasar Olympics ta nakasassu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Najeriya wasan wanda ya lashe zinare a gasar Paralympics

A 1992 ne Najeriya ta fara shiga gasar wasannin Olympics ta nakasassu, wato Paralympic a birnin Barcelona na Spain.

A lokacin dai ta tura 'yan wasa maza ne guda shidda, domin shiga wasannin guje guje da tsalle da daga nauyi da kuma kwallon tebur.

A wannan gasar dai Nijeriyar ta samu lambobin yabo na gwal guda uku, biyu a gudu daya a daga nauyi.

Tun daga lokacin, Najeriya ba ta taba fashin shiga gasar ba.