Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya

Image caption Jami'an tsaro a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya

A jahar kaduna da kuma wasu sassan Najeriya an fuskanci wani yanayi na alamun karin fahimtar juna da hadin kai tsakanin musulmai da kiristoci.

Hakan ya biyo bayan gayyatar da wasu al'ummar Musulmai suka yi wa kiristoci buda baki da ya wuce, yayin da wasu kiristoci kuma suka shiryawa musulmai buda baki, a lokacin azumin Ramadana da ya wuce.

To ko akwai wasu hanyoyi da za a bi domin ginawa a kan abin da aka gani a lokacin na azumi?

Shirin Gane Mini hanya na wannan makon ya tattaunawa da wasu masu ruwa da tsaki a bisa hanyoyin karfafa zaman lafiya a jahar kaduna.

Wakilin BBC a jihar Kaduna ne ya jagoranci tattaunawar.