Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Batun baiwa 'yan Najeriya damar mallakar makamai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hare haren bam na karuwa a Najeriya

A Najeriya yanzu haka ana cigaba da cece-kuce akan dokar mallakar makamai, inda wasu ke cewa, saboda tabarbarewar tsaro a kasar ya kamata a baiwa jama'a damar mallakar makamai.

Sai dai masu adawa da wannan matsayi na ganin cewa, yin hakan zai kara dagula al'amuran tsaron ne kawai.

To ko yaya kuke kallon wannan al'amari? kuma ko ta wacce hanya za'a shawo kan kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta?