BBC navigation

Zanga-Zanga a kan fim din batanci ga Musulunci

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:02 GMT

Zanga-zangar nuna fushi game da fim din da ya yi batanci ga addinin Musulunci

  • An cigaba da tashin hankali a yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afrika da kuma nahiyar Asia a kan fim din nan da ya yi batanci ga addinin Musulunci.
  • Ana nuna bacin rai ne ga Amurka, kasar da aka shirya fim din. A babban birnin Indonesia wato Jakarta, kamar sauran gurare da dama, masu zanga-zanga sun cinna wa tutar Amurka wuta.
  • A Srinagar, bangaren Kashmir dake karkashin ikon India, mata na kungiyar 'yan aware na cikin wadanda suka fito kan tituna don nuna fushinsu a kan Amurka.
  • A Sanaa babban birnin Yemen, jama'a ne suka yi ta la'antar Amurka, suna neman a kori jakadan Amurka dake kasar.
  • A birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan, daruruwan palasdinawa ne suka yi zaman dirshen don nuna fushinsu game da fim din.
  • Haka kuma a birnin Marawi dake kudancin Philippine kuma a tsibirin Mindanao, an yi zanga-zangar lumana game da fim din. Mutanen sun bayyana Amurka da Israila a matsayin makiyan Musulunci.
  • Wani dan jam'iyyar Azerbaijan Islamic party kenan, wasu 'yan sanda suka kama a Baku, saboda zarginsa da shiga wata zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Amurka.
  • Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga a kofar sansanin sojin Amurka a Kabul, babban birnin Afghanistan. Boren daga bisani ya juye na tashin hankali. Masu boren na bukatar a kashe wadanda ke da hannu a shirya fim din,

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.