BBC navigation

Gane Mini Hanya: Yaki da cin hanci da Rashawa

An sabunta: 24 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 12:06 GMT

Garmaho

Jami'ar Cambridge dake Ingila ta shirya wani taron karawa juna sani dangane da dabarun yaki da cin hanci da rashawa da kuma hanyoyin da za a bi wajen dakile laifukan da suka shafi yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Shugaban EFCC a Najeriya, Ibrahim Lamurde

Shugaban EFCC a Najeriya, Ibrahim Lamurde

A kwanakin baya ne Jami'ar Cambridge dake Ingila ta shirya wani taron karawa juna sani dangane da koyon dabarun yaki da cin hanci da rashawa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen dakile laifukan da suka shafi yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Taron wanda aka gudanar da shi a London, ya sami halarcin wakilan Kasashe sama da 40, inda kowacce kasa ta gabatar da kasida dangane da irin nata dabarun.

Shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da kuma muggan kwayoyi ta majalisar wakilan Najeriya, Jagaba Adams Jagaba na daya daga cikin wakilan da suka halarci taron da jami'ar ta cambridge ta shirya daga Najeriya.

Bayan taron kuma ya kawo ziyara ofishinmu dake London inda Ibrahim Mijinyawa ya tattauna da shi a kan irin abubuwan da zai ce Najeriyar ta koya daga taron.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.