Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hana wasu matan Najeriya shiga Saudi Arabia

Hakkin mallakar hoto AFP

A duk shekara dai Musulman da Allah ya horewa a ko'ina cikin duniya kan tafi aikin Hajji a kasar Saudiya, domin cika daya daga cikin shika-shikan musulunci 5.

Aikin Hajji dai na sa Musulmi ya san muhimmancin rayuwa a nan Duniya da lahira ta hanyar kawar da dukanin wasu sigogi na matsayi a cikin al'uma ko wadata ko kuma wata alfarma.

Ana gudanar da aikin hjji ne a watan Dhul Hijjah wanda shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci.

Tafiya ce ta ibada da kowane musulmi baligi dake da hankali kan yi akalla sau daya a rayuwarsa, idan yana da hali da kuma lafiyar yi.

A duk shekara dubban Mahajjata daga Najeriya ne ke zuwa wannan aiki na Ibada a Kasar mai tsarki.

Kuma a kusan kowace shekara aikin kan zo da kalubale daban daban ga mahajjata da kuma hukumomin kasar.

A bana an fara jigilar mahajjatan Najeriya zuwa Saudiyar ne kusan makwanni biyun da suka wuce.

Sai dai fara aikin jigilar ke da wuya wata matsala ta kunno kai, inda Jami'an shige da Ficen Baki na Saudiya, suka soma rarrabe mata da maza, suna tsare matan na Najeriya.

A cewar jami'an, matan wadanda ke da matsakaitan shekaru ba sa tare da muharramansu.

Yanzu haka dai wannan matsala ta fara shafar huldar diplomasiyar tsakanin kasashen 2, bayan da hukumomin Saudiyar suka tisa keyar matan fiye da dubu daya zuwa Najeriya.

To ko yaya jama'a ke kallon wannan al'ammari?

Me ya kamata a yi don kaucewa shiga cikin irin wannan matsala a nan gaba?

Kadan kenan daga cikin irin batutuwan da muka tattauna a kai a Filin na Ra'ayi Riga: