BBC navigation

Ra'ayi Riga: Hana wasu matan Najeriya shiga Saudi Arabia

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:51 GMT

Garmaho

Filin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tattauna ne kan matakin da kasar Saudiyya ta dauka na hana wasu maniyyata daga Najeriya gudanar da aikin hajjin bana saboda rashin zuwa tare da muharramansu.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Mata Mahajjata

A duk shekara dai Musulman da Allah ya horewa a ko'ina cikin duniya kan tafi aikin Hajji a kasar Saudiya, domin cika daya daga cikin shika-shikan musulunci 5.

Aikin Hajji dai na sa Musulmi ya san muhimmancin rayuwa a nan Duniya da lahira ta hanyar kawar da dukanin wasu sigogi na matsayi a cikin al'uma ko wadata ko kuma wata alfarma.

Ana gudanar da aikin hjji ne a watan Dhul Hijjah wanda shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci.

Tafiya ce ta ibada da kowane musulmi baligi dake da hankali kan yi akalla sau daya a rayuwarsa, idan yana da hali da kuma lafiyar yi.

A duk shekara dubban Mahajjata daga Najeriya ne ke zuwa wannan aiki na Ibada a Kasar mai tsarki.

Kuma a kusan kowace shekara aikin kan zo da kalubale daban daban ga mahajjata da kuma hukumomin kasar.

A bana an fara jigilar mahajjatan Najeriya zuwa Saudiyar ne kusan makwanni biyun da suka wuce.

Sai dai fara aikin jigilar ke da wuya wata matsala ta kunno kai, inda Jami'an shige da Ficen Baki na Saudiya, suka soma rarrabe mata da maza, suna tsare matan na Najeriya.

A cewar jami'an, matan wadanda ke da matsakaitan shekaru ba sa tare da muharramansu.

Yanzu haka dai wannan matsala ta fara shafar huldar diplomasiyar tsakanin kasashen 2, bayan da hukumomin Saudiyar suka tisa keyar matan fiye da dubu daya zuwa Najeriya.

To ko yaya jama'a ke kallon wannan al'ammari?

Me ya kamata a yi don kaucewa shiga cikin irin wannan matsala a nan gaba?

Kadan kenan daga cikin irin batutuwan da muka tattauna a kai a Filin na Ra'ayi Riga:

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.