BBC navigation

Gasar zane-zanen gidaje na duniya

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 09:01 GMT

Gasar zanen gine-gine na duniya

 • Fiye da gine-gine 300 ne daga bangarori daban-daban aka kebe a matsayin wadanda za su shiga gasar zanen gine-gine na duniya. Inda za a zabi wadanda za su lashe gasar a a bangarorinsu , kafin daga bisani su yi goyayya da juna, sannan kuma a zabi wanda zai lashe gasar baki daya. Wannan wasu benayen gidaje ne, kafa miliyan biyu da aka gina a bakin ruwa na Keppel Bay dake kasar Singapore.
 • Wajen baje- kolin hotuna na Vanke Triple V, a bakin ruwan Dong Jiang a Tianjin dake China.
 • Shalkwatar iGuzzini a Spaniya, wanda kamfanin masu zanen gini na MiAS ya zana. Gurin dai cibiya ce ta habaka fasaha da kwarewa wajen samar da na'oirin wutar lantarki.
 • Wannan ginin da McBride Charles Ryan ya zana ne, kuma an gina shi ne a arewacin Fitzroy a Melbourne, babban birnin Australia.
 • Gidan ajiye kayayyakin tarihi na bangaren ilimin likita da kirkire-kirkire na Paul S Russell, an gina shi ne a asibitin jami'ar Massachusetts dake Amurka.
 • Gidan nuna wasannin kwaikwayo na Soweto, an gina shi ne a Jabulani. Daya daga cikin muhimman dalilan gina wannan gida shi ne don samarwa mutanen Afrika ta kudu gurin da ake harkokin wasannin kwaikwayo.
 • Soundforms Shell na BFLS dake Docklands a London, guri ne da ake yin wakoki.
 • Nan wani gurin yin taro ne a bayan ginin Matiatia dake bakin ruwa a tsbirin Waiheke a New Zealand.
 • Cibiyar yada al'adun gargajiya dake birnin Yurihonjo a kasar Japan. Gurin ya hada da wajen nuna wasannin kwaikwayo da dakin karatu da kuma wajen yin taro na mazauna birnin.
 • Gidan Silima na farko da Coop Himmelblau ya zana a Koriya ta Kudu.
 • Gidan ajiye kayan tarihi na zane-zane na Sven-Harry dake Stockholm a Sweden.
 • A shekarar 2008 ne RYRA Studio ya zana wannan wurin shakatawar a Tehran, babban birnin Iran. Za a yi gasar zanen gine-gine na duniyar ne a Singapore daga ranar uku ga wata zuwa biyar ga watan Octobar shekarar 2012.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.