Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za a fito da iPad Mini a tsakiyar watan Oktoba

Mai yiwuwa a fitar da sabuwar na'urar iPad karama a tsakiyar watan Oktoba. Na'urar, wacce watakila za a sanya mata suna iPad Mini, za ta fito da fuska wacce ba ta karasa inci takwas ba. Ana kuma sa ran Samsung Galaxy III ma za ta kankance, yayin da ake zuba ido a ga samfurin wayar mai fadin inci hudu.