Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu: Wa zai auri 'ya ta na ba shi miliyoyin daloli_Attajiri

Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Mr. Cecil Chao da 'yarsa Gigi

Wani hamshakin mai kudi a Hong Kong, Cecil Chao na neman wanda zai auri 'yarsa, Gigi Chao ya kuma bashi dalar Amurka miliyan 65.

Attajirin dai yace bai damu ba mutumin ko mai arziki ne ko kuma talaka ne.

Tallar ta biyo bayan samun labarin da Mr. Chao ya yi na cewa 'yarsa ta auri wata kawarta Sean Eav.

Shirinmu na Taba kidi Taba Karatu na dauke da karin bayani game da wannan labarin da ma wasu masu kayatar wa da ban mamaki ko ban haushi.