Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tabarbarewar asibitocin kwakwalwa na Ghana

BBC ta gano mummunan yanayin da wata cibiyar kula da masu tabin hankali ke ciki a Accra, babban birnin kasar Ghana.

Mun samu shiga daya daga cikin cibiyoyin da wani rahoto na kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ya ambato, don nuni da irin mummunan yanayin da wadansu cibiyoyin kula da masu tabin hankali uku ke ciki a Ghana.

Rahoton ya yi bayanin yadda marasa lafiya kan zauna babu abinci, da yadda ake garkame su, da kuma ukubar da ake gana musu.

Mai yiwuwa wasu daga cikin hotunan da za ku gani su daga muku hankali.