Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ci gaban da mata ke samu a nahiyar Afrika

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Shugabar kasar Liberiya, Ellen Jonhson-Sirleaf

A cikin 'yan shekarun nan mata a kasashen Afrika na samun karin dama a fannoni daban daban da suka hada da sha'anin mulki, kuma yanzu haka ma akwai mata da dama dake rike da manyan mukamai a fannoni daban daban a kasashen Afrika.

Sai dai duk da haka kusan za'a iya cewa, an bar matan a baya ta fannoni da dama a nahiyar , inda alkaluma ke nuna cewa, har yanzu mata ba sa samun damar da ta kamata wajen taka rawa a gudanar da al'amurran kasa.

Alkaluma na nuna cewa, kashi biyu bisa uku na mata a kasashen Afrika ne ba su iya karatu da rubutu ba, kuma kashi saba'in cikin dari na mutanan dake fama da talauci a nahiyar Afrikan mata ne.