BBC navigation

Ci gaban da mata ke samu a nahiyar Afrika

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:03 GMT

Garmaho

A cikin 'yan shekarun nan mata a kasashen Afrika na samun karin dama a fannoni daban daban da suka hada da sha'anin mulki, inda yanzu haka akwai mata da dama dake rike da manyan mukamai a Afrika, ciki har da shugabancin kasa.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Shugabar kasar Liberiya, Ellen Jonhson-Sirleaf

Shugabar kasar Liberiya, Ellen Jonhson-Sirleaf

A cikin 'yan shekarun nan mata a kasashen Afrika na samun karin dama a fannoni daban daban da suka hada da sha'anin mulki, kuma yanzu haka ma akwai mata da dama dake rike da manyan mukamai a fannoni daban daban a kasashen Afrika.

Sai dai duk da haka kusan za'a iya cewa, an bar matan a baya ta fannoni da dama a nahiyar , inda alkaluma ke nuna cewa, har yanzu mata ba sa samun damar da ta kamata wajen taka rawa a gudanar da al'amurran kasa.

Alkaluma na nuna cewa, kashi biyu bisa uku na mata a kasashen Afrika ne ba su iya karatu da rubutu ba, kuma kashi saba'in cikin dari na mutanan dake fama da talauci a nahiyar Afrikan mata ne.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.