Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga; Zargin cin zarafin jama'a a Borno da Yobe

Image caption Jami'an tsaron Nijeriya

A Najeriya mazauna biranen Maiduguri da Damaturu na ci gaba da zargin rudunar tsaro ta JTF da muzguna musu, da cin zarafinsu, wasu lokuttan ma har da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai jami'an tsaron na musanta wannan zargi, inda suke ikirarin cewa, ana kai musu hari amma jama'a ba sa ba su hadin kai wajen zakulo mutanen da ke kai musu harin.

Shin yaya kuke kallon wannan al'amari, kuma ina mafita daga wannan matsala?

Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na yau.