BBC navigation

Ra'ayi Riga; Zargin cin zarafin jama'a a Borno da Yobe

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:44 GMT

Garmaho

A Nijeriya, ana samun zargin kisa da cin zarafin jama'a da jami'an tsaro ke yi a jihohin Borno da Yobe, a yunkurin da suke na murkushe 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlil Sunna, da aka fi sani da suna Boko Haram.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Jami'an tsaron Nijeriya

Jami'an tsaron Nijeriya

A Najeriya mazauna biranen Maiduguri da Damaturu na ci gaba da zargin rudunar tsaro ta JTF da muzguna musu, da cin zarafinsu, wasu lokuttan ma har da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai jami'an tsaron na musanta wannan zargi, inda suke ikirarin cewa, ana kai musu hari amma jama'a ba sa ba su hadin kai wajen zakulo mutanen da ke kai musu harin.

Shin yaya kuke kallon wannan al'amari, kuma ina mafita daga wannan matsala?

Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na yau.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.