BBC navigation

Babbar Sallah: Kasuwannin dabbobi na wucin gadi a Najeriya

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 23:45 GMT

Babbar Sallah: Kasuwannin dabbobi na wucin-gadi a Najeriya

  • Wani kosasshen ragu a daya daga cikin kasuwannin wucin-gadi na birnin Kano. Wasu da suka so yin layya dole ko dai suka hakura dungurungum, ko kuma suka sayi wanda bai kai wannan ba, wato ka-fi-zuru.
  • Wata kasuwar dabbobi ta wucin-gadi a Kaduna. Saboda yawan dabbobin da a kan kai birane a Najeriya, ba bakon abu ba ne a samu kasuwannin dabbobi na wucin-gadi a gefen tituna da unguwanni.
  • Ba raguna kadai a kan kai kasuwannin dabbobi na wucin-gadi ba. A nan wata kasuwar shanu ce ta wucin-gadi a birnin Kanon Dabo da ke Najeriya.
  • Wata kasuwar raguna ta wucin-gadi a birnin Kano na Najeriya. Kasuwannin dabbobi a fadin birnin Kano dai ba su da yawa, don haka idan Sallah Babba ta gabato sai a kakkafa na wucin-gadi irin wannan a unguwanni.
  • Wasu raguna da aka kange a wata kasuwar wucin-gadi da ke jikin wani gida a Kaduna. Sai dai a birnin na Kaduna wani mai sayar da raguna ya yi rashin sa'a: ya hadu da 'yan damfara wadanda suka kwashi raguna goma sha biyar suka ba shi dalar Amurka jabu.
  • Masu hannu da shuni ga naku. Amma sauran mutane ma, musamman masu watanda, su kan sayi shanu da zarar Sallah Babba ta gabato.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.