BBC navigation

Ra'ayi Riga: Yaushe 'yan Afruka za su ci gajiyar dimbin albarkatun kasar da Allah ya hore ma su?

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:41 GMT

Garmaho

Allah ya wadata nahiyar Afurka da dimbin albarkatun kasa. Sai dai duk da haka, ga alama galibin jama'ar nahiyar na fama da tallauci. To ko me sa hakan? Ta yaya kuma 'Yan Afruka za su ci gajiyar wannan arziki?

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Wani wurin hakar mai a cikin teku

Wani wurin hakar mai a cikin teku

Allah ya albarkaci Afrika da dimbin arzikin kasa, ko da a shekarar da ta gabata an gano sababbin manyan albarkatun kasa a kasashen Afrika da yawa.

Daga cikin su akwai Kwal da mai da iskar gas a kasashe kamar Kenya da Tanzania da Mozambique da kuma Uganda. Ghana ta soma hakar mai a cikin watan Disamba 2010, kuma ta kara gano wani man a gabar tekun yammacin Afrika.

Ita ma Jamhuriyar Nijar baya ga arzikin ma'adinin Uranium, ta fara taace manta a cikin watan Nuwamban bara.

Najeriya dai tana cikin kasashen dake kan gaba wajen fitar da mai zuwa kasuwannin duniya tsawon shekaru da dama, amma kuma akasarin al'ummar Najeriyar na fama da kangin talauci.

To ko sai yaushe ne al'ummar Afurka zasu ci gajiyar wannan dimbin arziki da Allah ya horewa kasashensu? Kuma ko me ya sa ake karkata dimbin arzikin da ake samu daga mai da uranium, da zinare, da sauransu zuwa aljihun wasu 'yan tsiraru a kasashen Afurka da dama?

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.