BBC navigation

Rikicin Musulmi da mabiya addinin Buddha a Burma

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:10 GMT

Rikicin Musulmi da mabiya addinin Buddha a Burma

 • Musulmi 'yan gudun hijira dauke da kayansu lokacin da suka isa garin Sittwe, Jihar Rakhine, a yammacin Burma, ranar Lahadi 28 ga watan Oktoba shekarar 2012. Kananan jiragen ruwa ne suka kawo wadansu daga cikin mutanen da suka tsere babban birnin jihar ta Rakhine.
 • A nan ana iya ganin Musulmi daga garin Kyaukphyu a Jihar Rakhine wadanda suka tsere zuwa Sittwe kwanaki kadan da suka gabata sanadiyyar tashe-tashen hankula a gabar Thechaung kusa da garin na Sittwe ranar 28 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Jami'an 'yan sanda dauke da makamai a motarsu suna gadin wani sansanin 'yan gudun hijira a Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine, a yammacin Burma, ranar Asabar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Wani kwalekwale yana wucewa ta kusa da wani gidan da aka kona a garin Pauktaw da ke wajen garin Sittwe a yammacin Rakhine ranar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Wani soja da ke tsaye yayin da jama'a ke tattara karafa daga baraguzan wata unguwa a garin Pauktaw wadda aka kona a tashe-tashen hankula na baya-bayan nan ranar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Wani yaro dauke da jakar karafan da ya tattaro daga baraguzan wata unguwa a garin Pauktaw wadda aka kona a rikici na baya-bayan nan ranar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Wata yarinya wadda ta bi sahun sauran jama'a wajen tattara karafa daga baraguzan wata unguwa a garin Pauktaw wadda aka kona a rikici na baya-bayan nan ranar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Wani dan sanda dauke da makami yana gadin Musulmi 'yan gudun hijira a wani sansanin 'yan gudun hijira da Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine, a yammacin Burma, ranar Asabar, 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • Sojojin Burma a wani wurin bincike a Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine, a yammacin Burma ranar Asabar 27 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • A wannan hoto da aka dauka ranar 9 ga watan Oktoba, shekarar 2012, ana iya ganin mabiya addinin Buddha 'yan kabilar Rakhine a wurin bauta na Shwe Zaydi wanda aka mayar sansanin 'yan gudun hijira a Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine da ke yammacin kasar Burma.
 • A wannan hoto da aka dauka ranar 25 ga watan Oktoba, shekarar 2012, ana iya ganin wani dan gudun hijira dan kabilar Rakhine yana shan abin sha yayin da ake duba lafiyarsa a Kyauktaw, Jihar Rakhine.
 • Wani dan kabilar Rakhine mai bin addinin Buddha a kwance a wani asibiti da ke Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine ta yammacin Burma ranar 26 ga watan Oktoba, shekarar 2012.
 • A wannan hoto da aka dauka ranar 11 ga watan Oktoba, shekarar 2012, ana iya ganin Musulmi 'yan kabilar Rohingya a sansanin 'yan gudun hijira na Say Thamagyi da ke wajen Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine.
 • A wannan hoton da aka dauka ranar 10 ga watan Oktoba, shekarar 2012, ana iya ganin Musulmi 'yan kabilar Rohingya a wata makarantar Islamiyya ta 'yan gudun hijira a wajen Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine da ke yammacin Burma.
 • A wannan hoton da aka dauka ranar 11 ga watan Oktoba, shekarar 2012, ana iya ganinMusulmi 'yan kabilar Rohinya suna wucewa ta hanyar zuwa sansanin 'yan gudun hijira na Say Thamagyi wadda ambaliyar ruwa ta rufe, a wajen Sittwe, babban birnin Jihar Rakhine.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.